Namiji
Daga cikin tambayoyin da ke zukatan mata, amma ba su cika furta su ba, akwai: “Wa ne namiji?” Tambayar da kuma ta yi kama da wasa, amma tana da muhimmanci, musamman a wurin Matan. Haka nan, ta yi kama da sassauka, amma tana da wuya, musamman in za a danganta ta da zamantakewar iyali. “Idan ka so yi wa wannan tambaya dukan-falen-d aya, ko shan ruwa ya fi ta wuya. Domin daga ka ce: “DanAdam, wanda ba jinsin mata ba ne.” ka gama amsawa. Sai dai kuma daga jin yadda idan ana magana wataran Bahaushe kan ce: “Ai wane namiji ne!” To za ka tabbata cewa kalmar tana da fadin ma’ana fiye da gurbin da waccan amsar ta sama za ta iya cikewa. Ashe kenan akwai sauran aiki a gaba. Domin kalmar ta fi karfin a yi mata kwaf-daya, kamar yadda muka zata. Da ya ke a wannan fage ana tattaunawa game da abin da ya shafi zamantakewa da alakar mace da namiji ne, bari mu kalli kalmar Namijin ta irin wannan mahanga: A wannan fage, idan aka ce Wa ne Namiji? Ba wai kana bukatar banbanci jinsi kadai ba ne. A’a, ana bukatar ka dauki mutum ka aza shi a wani sikeli ne, sai ya kai adadin wani nauyi, sannan ka ce “E, wannnan Namiji ne. Idan ko ya gaza, sai ka ce “Wannan jinsin maza ne.” Za kuma mu iya samun duk rigunan da Namijin zai sa, wadanda za su kara mar nauyi su kuma fito da kamannin da suke nuna kamalarsa ta cika namiji ne daga nassosi da kuma mahangu na zamani. Kasancewarmu Musulmi ina ganin zai fi dacewa mu fara kallon kalmar tun daga cikin Alkur’ani. Wato mu kalli ayar nan da ta shahara a bakin kusan kowane namiji, yayin da ya tashi nuna fifikonsa a kan mace: Ina maganar aya ta 34 a cikin Nisa’i. Hakika kamar yadda ayar ta tabbatar Ubangiji madaukaki ya fifita maza a kan mata, Ya sanya su su ne matsaya kuma madaukaka a bisan mata. Wannan batun kuwa haka yake ba mai iya musanta shi. Domin ko kallon yanayin zamantakewar rayuwar da ake gudanarwa tsakanin mace da namijin ka yi, ta ishe ka tabbatar da wannan batu. Watakila kuma shi ya sa har mutanen ma da ilimi bai riske su ba suke tafe kan wannan tsari, na daukaka da darajta maza burbishin mata. Sai dai fa Malamai suna cewa; duk inda ka ji an ce “Bi..” ko “Bi ma.” To, bayanin da zai biyo, shi ne tafsirin dunkulallen zancen da aka yi a baya. Kenan, a wannan aya da ke nuna fifikon maza, akwai bukatar bayan namiji ya ji ta, ya ji a ransa cewa ya na sama da mace, to ya kuma bibiyi dalilan da suka sa aka ce yana sama da macen, wadanda ke hade a jikin ayar. Wato: “Bi ma faddhalallahu ba’adhuhum alaa ba’adhin, wa bi ma amfaku min amwalihim.” Malaman tafsiri sun ce akwai abubuwa da dama dunkule a cikin wannan gabar. An dai ambaci abin da ya shafi dawainiyar ciyarwa da sauran lamuran dake bukatar kudi karara, amma abubuwan da ba a ambata ba din kamar su ilimi,hankali,jarumta,juriya dasauransu sun ma fi yawa. Ka sami wani malamin yai ma sharhin ayar, ka ji. Kowane abu dama yana da dalili, wadannan tarin dalilai su ne suka sa namiji ya fi mace. To ko akwai wani juyi da za a yi wata macen ta zo ta fi namiji? To, tunda dai akwai dalilan kasancewarsa hakan, ina ganin ba laifi mu aro wani ma’auni ko sikeli da Malam ya kawo a cikin littafin Ta’alimi. Wanda ake auna cikar mutum. Inda a cikinsa aka raba mutane ko mazaje (tunda da kalmar rijaal akai amfani), zuwa gidaje uku. Wato akwai: 1, mutum, akwai 2 rabin mutum, akawai kuma ma 3 wanda ba komai ba ne, wato shi ba ma a sa shi a lissafin cikakkun mutane. To da ya ke mu kuma za mu nufi gidan aure ne kai tsaye, ya ya kamata mu auna namiji bisa danganta shi da matarsa ko halayyarsa a yayin mu’amularsa da mata? Watakila hanya mafi sauki da za mu bi wurin aunawa shi ne, mu ma dai mu aza su kan waccan humular, amma sai mu ce: Akwai 1 Namijin da ya fi mace, da 2Namijin da yake daidai da mace, da kuma 3 Namijin da bai kai mace ba. Bari in yi kokarin aza ka a bisa hanya, ya kai maikaratu, alabasshi daga nan kai ma ka je ka ci gaba da bincike ko nazarin sahihancin batun. Aiki ya same ka kai ma. Namiji Wannan shi ne wanda ayar can ta nufa kai tsaye. Ina nufin akwai cikakken namiji a cikin maza. Wanda ya ke da wadancan nagartoci da ayar ta kunsa. Wato ,Namiji wanda yake daukar dawainiyar gidansa. Yake kuma da kaifin hankali da ilimi da azancin rarrabe tsanin aya da tsakuwa yayin da abubuwa suka cakude. Domin kowane namiji shugaba ne ko a gidansu ko a gidansa. Saboda haka ne dolensa cikin abubuwan da ake sa ran ya siffantu da su don cikarsa namiji, akwai wadannan suffofi na alkalanci. Ba ka lura ba ne, duk rikicin da ya faru a gidanku Mahaifinku ne yake yanke hukunci ko yin sulhu ba? Dole ne kuma namiji ya zama mai jarumta da juriya da gwarzontaka. Ta yadda dukkan wata damuwa da za ta doso gidan ko wani abin tsoro, shi ake tsammanin zai wuce gaba yai Uwa yai Mawankiya. Ba ka ga idan Mahaifiyarka da Yayyu da kannenka mata duk suna cikin gida kadangare ya shigo gidan duk kai za su ce ka zo ka fitar musu da shi ba? Dole ne ya zama jajirtacce wurin neman abinci da sauran dukkan wata bukata da ka iya tasowa a gida, wato daukar nauyi ko dawainiyar gida baki daya. Babu wani namiji da ake tsammanin ya zauna ya nannade kafa, matarsa ko dangi su rika ciyar da shi. Komai arzikinta kuwa. Dama sanannen abu ne cewa cikin sharudan da Liman kan bayar a gaya wa Ango tun kafin ya ida daura musu aure, sai ya ce: “ To ci da sha da tufatarwarta duk suna kansa.” Bayan walinsa ya amsa ne ta hanyar gyada kai ko furuci, sannan a daura auren. Watakila da zai ki amsawa da sai dai a ba wa mutane hakuri, cewa su tafi, an daga daurin auren. Kai ma ba ka gani ba, kullum Baba shi yake fita ya nemo? To wadannan suffofi da dange-dangensu, su ne idan mutum ya siffantu da su za a iya ce mar Namiji. Wanda Ya Ke Daidai Da Mace Amma Namijin da yake daidai da mace, shi ne Namijin da ya aro dabi’un da suka fi suffantuwa da na mace, yayin da ya kuma rasa kaso mafi tsoka na suffofin namijin. Kodayake ba kasafai hankalinmu yake kaiwa ga irin wadannan mazan ba, watakila saboda cakudewar lamura da rikicewar zamani. Sai da yawa sai abubuwa su yi ta faruwa a gabanmu ba tare da mun tsaya mun yi musu karatun-ta-nutsu ba. Amma a wannan zamani wannan rukuni ya yi awon gaba da kaso mai tsokar gaske cikin al’umar Hausawa. Wadannan suffofi su za mu zayyana gwargwadon iko a mako mai zuwa in sha Allahu.
https://mujallarfilm.blogspot.com/2019/01/namiji.htmlhttps://mujallarfilm.blogspot.com/2019/01/namiji.html
https://mujallarfilm.blogspot.com/2019/01/namiji.htmlhttps://mujallarfilm.blogspot.com/2019/01/namiji.html

Leave a Comment