Fina-Finan Kannywood 10 Da Suka Yi Fice A 2018
Jami’ar Cologne
Allah Ya kara kawo masana’antar Kannywood zuwa karshen wannan shekara.
Ba ma wannan kadai ba, masana’antar ta samu ci gaba da har ta yi fina-finai iri-iri, wadanda yawanci na barkwanci da soyayya ne, da kuma almara, wadanda kalilan ne.
Daga ciki akwai fim din ban-dariya na Adam A. Zango, wato Dan Kuka a Birni da fim din Ali Nuhu da ya yi shi shekara 18 baya kuma ya sake yinsa yanzu, Mujadala, da dai sauransu.
Kabiru Jammaje, wanda shi ne musabbabin farfadowar sashen Ingilishi a Kannywood, ya sake daukar nauyin wani kasaitaccen fim din sarauta mai suna In Search of the King.
Da alamun fim din Nafisa Abdullahi, Yaki a Soyayya, ma za a ji dadinsa, saboda haka shekarar ta 2018 ta kayatar.
Wadannan fina-finan da aka jero a kasa su ne suka fi shahara da fice a wannan shekarar, wacce ta zo dab da babban zaben Najeriya wanda za a yi farkon shekara mai zuwa.
Ga shi siyasa ta kunno kai cikin masana’antar ta Kannywood, har ma ake ganin ta janyo rarrabuwar kawuna gami da barazanar kara raba kan mambobin masana’antar da ba a jima da sasanta su ba – kodayake, wannan ba shi ne maudu’inmu yanzu ba.
Fina-finan ba bisa daraja aka jera su ba:
1. Ruwan Dare
Ruwan Dare ne ya yi fice a cikin fina-finan Kannywood na 2018Fim din, wanda daraktansa shi ne Yaseen Auwal kuma ake ganin yana daya daga cikin fina-finan Kannywood da suka fi dacewa da yanayin da ake yanzu, yana shagube ne cikin salon tsoratarwa ga matasan da suka gama jami’a kuma suke raina duk wani aikin da ba na ofishi ba.
Aminu Sharif, wato Momoh, da Sadiq Sani Sadiq wasu mutane ne da suke son yin kudi ko ta wane hali kuma masu tsananin buri ne, wadanda sun gama digirinsu na farko a fannin Akanta da Tattalin Arziki.
Abokinsu kuwa, wanda shi ma ya gama jami’ar, Baballe Hayatu, ba irin salonsu ya dauko ba.
Saboda haka, daga karshe sai ya samu nasara.
Su kuma wadancan biyu daga karshe sun koyi darasi sannan suka yi nadama.
Fim din ya yi matukar haduwa saboda yadda jigonsa yake da alaka da wannan zamanin.
Kuma ‘yan wasan, wadanda aka ambaci sunayensu a sama da ma wadanda ba a ambata ba, sun yi kokari sosai.
Za a iya kau da kai daga ‘yan kura-kuran cikin fim din – irin su ambatar Yugoslavia a matsayin kasa, kura-kuran nahawun Turancin Ingilishi, da sauransu.
2. Rabi’atu
Maryam Yahaya a fim din Rabia’atuRabi’atu, wanda Aminu S. Bono ya yi darakta, an shirya shi ne kwata-kwata a gidaje guda uku; kuma yana nuna irin hadarin da ‘yar aikin gida ke shiga a gidan da take aiki.
Maryam Yahaya, wacce ta fito a matsayin ita ce Rabi’atu, takan yi duk aikace-aikacen babban gidan Alhaji Rabiu Rikadawa, yayin da matarsa, Hadiza Muhammad, kuwa ke zuwa wajen aiki; ‘ya’yansa hudu kuma makaranta suke zuwa.
Rabi’atu dai yarinya ce mai yarinta kuma kamammiya, wacce gidansu ba masu karfi ba ne.
Saboda haka kowa a cikin gidan da take aiki sonta yake yi, har ma manyan ‘ya’yan gidan guda biyu suke takara da juna wajen samun karbuwar soyayya a wajenta.
Sai dai ba ta amince da su ba, tana mai jaddada musu cewa sun wuce ajinta.
Sai dai duk da haka ba wanda ya hakura a cikinsu.
Ana haka, kwatsam sai wata rana Alhaji ya zo gidan ya same ta ita kadai har ya yi lalata da ita.
Daga bisani, sai matar Alhaji ta gano Rabi’atu fa ta samu juna-biyu sakamakon lalata da Alhaji ya yi da ita.
Aka yi ta gumurzu dai har zuwa karshe.
Fim din bai ci kudi ba, amma ya yi matukar dacewa da yanayin da ake ciki yanzu.
Sannan, labarin ya yi kama da zahiri kuma daraktan da mataimakansa da kuma ‘yan wasan, wadanda ba shahararru ba ne, sun yi aiki da basira sosai.
Babu rawa da waka a ciki.
Ba ma wannan ba, karshen fim din ya kayatar.
3. Fuska Biyu
Fim din Fuska BiyuFuska Biyu yana nusarwa ne game da yadda wasu iyaye ke saurin aurar da ‘ya’yayensu mata ba tare da bincike kan mazajen da za su aurar wa ba.
Fim din yana ba da labari ne na wani madugun masu garkuwa da mutane, Adam A. Zango, wanda da rana yake bayyana a matsayin mai sayar da kifi.
Amal, wata kamilalliyar yarinya, wacce ‘yan uwanta ba masu karfi ba ne, takan sayar da abinci a gefen teburin da Zango ke ikirarin yana sayar da kifi.
A haka sai suka fara soyayya.
Irin abin duniya da yake ba ta ya sa mahaifiyarta take jin akwai lauje cikin nadi.
Amma mahaifinta kuma ya dage cewa ‘yarsa fa ta samu mijin aure.
Sai kuma da lokaci ya kure sannan mahaifin ya fahimci kuskurensa.
Fim din akwai jan hankali cikinsa.
Yana da amfani sosai a kalle shi.
4.Risala
Fim din RisalaSunan wannan fim, Risala, wata kalma ce ta Larabci, wacce ke nufin “sako”.
Risala, wanda Abubakar S. Shehu ya yi darakta, siffofin zamanin baya yake da su.
Gogaggen tauraron nan, Sadiq S. Sadiq (Zakariyya), ya yi wata tafiya da nufin neman mutumin da ya yi wa ba-daidai ba don neman afuwa.
Tafiya ce mai cike da karaskiya, masifu da abubuwan al’ajabi.
Abin bai tsaya a haka ba – sai da ya sake haduwa da wata jarrabawa a wani gari da ake kira Baihan, garin da mutumin yake.
Wannan mutumin ya yarda zai masa afuwa amma sai in ya amince zai auri ‘yarsa, wacce, a cewarsa, ta fi kowa muni a garin kuma musaka ce.
Sai Zakariyya ya amince amma ba cikin son ransa ba.
Ashe dai yarinyar nan ba haka take ba; hasali ma, yarinyar matukar kyau ne da ita.
Bayan ‘yan kura-kurai da fim din ke da su kamar rashin takaita darussa da yake koyarwa, da kuma ci-da-karfi wajen aiwatar da wasu abubuwa, fim din ya dauko tarihin haihuwar shahararren malamin addinin Islaman nan ne, Abu Hanifa.
Kodayake yawancin fina-finan Kannywood kwaikwayo su ake yi daga wani waje.
Baya ga haka, sautin shirin ya dauku.
5. Hakki
Fim din HakkiKamar yadda ake fada, tsohuwar zuma da ita ake magani.

Leave a Comment