Bayanin Ciwon Sanyi Mai Suna (Candidiasis)

Ita dai wannan ciwo da turawa suka kira ta da ‘Candidiasis’ wato ‘Mardhul fidriyyat al’unkudiyyah, ciwon sanyi na ‘Kandida’ an gano shi a shekara ta 1849 mld. Kuma ya fi damun mata, la’alla ko don jikinsu a dude yake, shi ya sa ma da wuya mace ta gama rayuwarta ba ta kamu da shi ba. Saboda mata suna saurin daukarsa a bandaki ko wurin haifuwa. Mace in ta samu ciki jikinta yana kara budewa wato farjinta, shi ya sa za ka ga mata masu ciki suna yawan fama da shi, su dinga ganin farin ruwa a gabansu. Ko da yake akwai wani nau’in ciwon sanyin da shi ba daukarsa ake ba ta cikin jiki yake haifuwa sakamakon gurbacewar jiki, sai ka ga ana ta ganin farin ruwa a gaba, wani lokacin kamar koko wani lokacin kamar tumbudi, wani lokacin kamar majina, yak an yi waria wani lokacin, har ma da kaikayi abinda bai kamata a samu a jikin mace ba ko alama. Amma su mata su kan rude suna tsammanin ai gaban mace dole ne ya yi irin wannan farin ruwan, wanda ko ba haka bane. Ruwan da ake samu a gaban mace ana cemasa danshi, wato ya kasance cikin gabanta ko yaushe da akwai laima, amma wacce ba ta da kala, yadda ka san ruwa kuma ba yauki, sannan ba ya kwarara har sai lokacin da ta sadu da sha’awa ko yaya take a barci ne ko a farke, sannan maziyyi ya zo, wanda shi kuma fari ne kamar kalar ruwa amma mai yauki kamar Kalkashi, wanda haka ake so a tattare da mace. Sannan lokacin da ta sadu mijinta ko wani dalili ya sa ta jin dadi ko ta yi mafarki, to sai maninyyi ya zo, wanda shi kuma wajen fitarsa akwai jin dadi, wanda hakan ne ya banbanta da sauran. Shi ya sa wadda ba ta jin dadi yayin da suke saduwa da mjinta to lallai tana da babbar matsalar da take bukatar dole ta zo mu ba ta magani musamman in tana haihuwa ko bari, wato tana samun ciki ita kuma maniyyin nata ya kan zo da dan kauri, kuma ruwan kasa-kasa. Shi ne Mnazon Allah Sallallahu alaihi wasallama a wani Hadisi Nasa’i ya fitar dada Ummu Sulaimi da ta tambayi Manzo game da, idan mace mace tana bacci ta yi mafarkin saduwa, shin za ta yi wanka? Sai Manzo ya ce “Kwarai kuwa idan ta ga ruwa kamar yadda namiji yake gani, to sai ta yi wanka.” Shi ne ta kara tambayarsa “Shin yana yiwuwa ita ma mace ta ga maniyyi a gabanta?” sai ya amsa cewa “Kwarai kuwa, to in ba haka ba to ta ina ake samun kama?” wato idan mace ba ta da maniyyi ta ina ake samun da yayi kama da mamansa, in dai ba don haduwar maniyyinta da na mijinta ba?. Shi ne Manzo Allah ya ci gaba da cewa “Inna ma’arrajuli galzun abyadhu, wa ma’ulmar’ati rakieekun asfaru”. Wato maniyyin namiji mai kauri ne fari, na mce kuma tsinkakke ne ruwan kasa-kasa. Saboda haka idan na namiji ya daukaka akan na mace, to sai yaron ya yi kama da shi, idan kuma na mace ya daukaka akan na namiji, to sai yaron ya yi kama da ita. Shi ne Malamai suke cewa, da wannan ne ake Ijtihadi a yi kokari a hada magunguna don a taimaka wa mai son ya samu mace ko namiji, tun da an gane sirrin daga bakin Manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama, bakin da baya karya. Kamar yadda Imamu ya kawo wasu hanyoyi da ake yin hakan da iznin Allah, a cikin laittafinsa ‘Alidah fi asrarunnikah’ a takaice dai muna gane mace tana da maniyyi har ma ga kalarsa ruwan kasa-kasa, sai idan mace ‘Yuhashe’ ce to yana iya zuwa da kauri kuma fari, saboda in dai mace tana ganin farin ruwa a gabanta, to ya zama na ciwo, ya zama daga cikin cututtukan sanyin da muka yi bayani a baya, ko kuma sakamakon gurbacewar jiki ko na wanan Kandida dinne da muke bayaninsa, kuma ko wane akwai yadda muke maganinsa a warke da iznin Allah Ta’alah. Akwai wacce ta zo wurinmu a gigice da ‘yarta mai shekara hudu, cewa ta zo za ta yi mata wanka sai ta gabanta caba-caba da farin ruwa kamar babbar mace da tai wani abu da mijinta, don har wurin ya kumbura, gashi kuma suna tare ba wani wuri ta je ba. Shi ne na ce mata ta kwantar da hankalinta ba wata matsala bace, muka ba ta magani, kuma muka umarce ta da ta je ta binciki sauran ‘ya’yanta mata guda uku da suke gida wanda su kuma manya ne, inda ta ba mu labarin cewa, “Ai ta bincike su, sai dai da yake su manya ne suna da shi kamar yadda ko wace mace take da shi”. Muka ce mata a a su ma na su irin nata ne Candida, kuma duk sun dauke shi ne a bandakinsu. Sai ta ce, to in dai haka ne ita ma tana da shi, domin ba ta rabu da shi, dukkansu muka hada masu magani muka ba su, kuma suka warke da iznin Allah ta’alah, kamar ma ba su taba yi ba. Shi wannan ciwo na Kandida ya kan kama maza da suka dauka a wurin matansu, sai dai shi a mafi yawa bai fiya nuna alama a jiki ba, sai dai kadan ne ake samu suke dan jin zafi, wadanda sukai wani abu da iyalinsu, ko kuma dan wani farin ruwa ya fito daga gabansu musamman suna gama saduwa.

Read More at: https://hausa.leadership.ng/2018/11/02/bayanin-ciwon-sanyi-mai-suna-candidiasis/

No comments

Powered by Blogger.