Amfanin Ganyen Gwaiba Ga Lafiyar Dan’adam
Kasahe da dama kama daga Japan da United State da Indiya da Egypt da Chana da ma fi yawan kasashen bakaken fata na Nahiyar Afirca sun dauki shekaru tun a zamanin kakanni zuwa yau suna cin gajiyar maganin da ganyen gwaiba ke yi. Binciken masana sirrin tsirran itatuwa dana kimiya sun jima da bada tabbaci na musamman kan alfanun ganyen gwaiba. Ganyen yana dauke da wasu irin muhimman sinadarai masu zaman maganin wasu cuttuka a wannan zamanin. Ga Kadan Daga Cikin Su: Ganyen gwaiba na maganin gudawa kama daga manya da kuma kanana, gudawar na sanadin cin abinci ne ko wani abin sha da ya lalata ciki ko kuma shigar wasu kwayoyin cuta da makamancinsa. Idan kananan yara musamman wadanda ke shan mama sun kamu da gudawa to sai ita uwar ta nemi ganyen gwaiba ta wanke da kyau sai ta sabeta sai ta saka ruwa ta tafasa sai ta tace ruwan ta sha rabin kofi da safe da kuma rana bayan awa daya ko biyu sai a baiwa yaro mama ya sha, in sha Allahu gudawar za ta tsaya. Haka idan uwar ce ta kamu da gudawa ko duk wani mutum babba shi ma zai iya yin haka in sha Allahu zai ji dadin jikinsa. A ma fi yawa masu fama da saurin lalacewar ciki ko masu yawan zuwa bayan gari, idan suka rungumi shan shayin ganyen gwaiba to za su sami lafiyar ciki da sassaucin kumburinsa da kuma takaita yawan zuwa bayan garin. Masu fama da yawan sinadirran cholesterol -wannan ganyen na gwaiba yana daidata yawan cholesterol da ke a cikin jikin mutum wanda yawansa a cikin jini ba karamin illa ba ne. Sai a dinga amfani da ganyen gwaiba sau daya a kullum da safe bayan an karya. Cuttukan Fata-kamar kaikayi ko kuraje ko kazzuwa da salewar fatar jiki. Dan kanoma – Idan ana fama da basir mai kumbura ciki ko yawan tusa dama tsutsar ciki da kasala da sauransu. Kiba ko taiba: Masu fama da nauyin jiki ko katon ciki kuma suna bukatar rage nauyin ba tare da wata illa ba. Ciwon suga-kasar Japan sun tabbatar kuma sun yadda da ganyen gwaiba na kare barazanar kamuwa da ciwon suga bayan sun kaddamar da wani bincike a kan sa, haka kuma ana amfani da shayin wannan ganyen dan magance wannan ciwon. Shi dai wannan ganyen na gwaiba yana da wasu sinadirrai dake rage zukar nau’ukan suga nan guda biyu waton maltose da kuma sucrose ya taimaka dan samun daidaituwar suga a jikin dan’adam bayan an ci abinci. Binciken da aka gudanar an wallafa shi ne a cikin kasida mai suna “Nutrition and Metabolism” wanda suka bada daki-daki a kan wannan bayanin. Ciwon ciki a tafasa sai a sha rabin kufi a kullum sau uku. Ganyen Gwaiba na samar da saurin waraka ga mai fama da ciwo a jiki. Ganyen na kumshe da daruruwan Bitamin C wadanda ke karfafa aikin garkuwar jiki dan samun damar yaki da cuta. Ganyen na magance kumburin hanji. Shayin ganyen gwaiba na maganin taurin bayan gari mai wahalar fita. Amfanin Rai-Dore A Jikin Dan’adam Rai-dore wata karamar ciyawa ce wacce da harshen Turanci ake kira da coffee sena. A Germany suna kiranta da suna kaffee kassie. A kasar India tana da suna Kasounda. A China suna kiranta da Wang-Jiang Nan. A harshen faransanci ana kiranta da suna Bentamar. A yayin da a harshen Hausa ana kiranta da suna Rai- dore a Hausar wasu jahohi kamar a Sakkwato suna kiranta da suna “sanga-sanga”. Ita dai wannan ciyawar tana da sayyu da ganye da kuma diya, tana da tsayin da ya kai na mita daya da digo takwas (1.8m). Ganyen rai dore na da launin kore mai haske a sanda take girma’a yayin da idan ta kosa ganyen kan canza launi ya koma mai rowan kasa. Ciyawar takan fito ta girma a wasu dai-daikun wurare masu damshin sanyi kamar a gadina, bakin gulbi ko a cikin daji a lokutan damina. Tana fitowa sau uku a cikin shekara. Sananniyar ciyawace da aka dauki dimbin shekarru ana amfani da ita a kasashe da dama a fadin duniya kama daga India, Kudancin Amurka, Brazil, China, Germany, France, Jamaica da kuma kasashen nahiyar Africa. A kasar Hausa an fi amfani da ganyen wannan ciyarwa dan maganin zazzabin Typhod da kuma masu ciwon shawara. Sai dai amfanin wannan ciyawar ta fi gaban ananata. A kimiyance tana dauke da sinadiran dake maganin wasu kwayoyin cuta kamar su : funiculosin, kaempferol, lignoceric acid,linoleic acid,oleic acid, danthorin, kuercetin, physcon, obtusin, tannic acid, emodin, cassiollin, a phytosphanol, physcion, occidentol I,II. Maganin Da Take Yi : Saiwar ciyarwa tana maganin zafin dafi na cizon kunama da maciji da sauran kwari amma banda na mahaukacin kare. Idan an sha kananzir ko wani sinadari mai illatar da jiki dan’adam to sai a nemi saiwar a tafasa sai a sha kamin a ci abinci. A maganin karya tsafi, ana amfani da saiwar rai dore a tare da ciyawar anniya makomiya da sassaken cediya sai a rubuta wasu surori uku na cikin Alkur’ani mai girma a yi amfani da su na tsawon kwana 7 dan karya tsafi ko sihirin da aka yi wa mutum. Mai fama da ciwon jiyoji zai iya neman saiwar ya dafa da kyau a tare da saiwar gero ya rinka suraci da su. Mai fama da zazzabin typhod zai iya neman ganyen rai-dore sai ya dake a tare da gero a yi gumba a saka ruwan zafi a dama kamar kunu sai a rinka sha. (kunun rai dore). Haka kuma zai tafasa dukkanin ciyarwa tun daga saiwarta, ganyenta har zuwa diyanta sai a yi surace da ruwan, safe da kuma yamma. Mai fama da shawara ya nemi rai dore da kuma lemun tsami sai ya wanke da kyau ya tafasa sai ya dibi ruwan da duminsu yana wanka da su. Rai-dore na maganin malariya, sai a nemi ciyawar dukanta a hada da ganyen bedi a tafasa a yi surace ko a yi wanka da ruwan kamin su huce. A kasar Brazil suna amfani da rai dore dan maganin rashin lafiyoyi kamar na zazzabin cizon sauro, tarin tibi, matsalolin hanta. Suna kuma ciza ganyenta su tauna su shafa a kan wani rauni ko kurji. Tana maganin basir mai tsiro idan aka hadata da wata saiwar sai a markade a mai da su tamkar man shafi sai a rinka shafawa a wajen da tsiron yake. Ana dafa ganyen ko a shanya ganyenta idan ya bushe sai a gauraya da ganyen lalle a kwaba a yi amfani da su dan kara armashin fata. Ba a bukatar Masu juna biyu ko masu shayarwa su sha rai dore amma za su iya amfani da ita su yi surace idan da ciwon jiki, ko malaria. Amma kada su sha domin tana motsa mahaifa. Sannan idan mai shayarwa ta sha to shima yaron zai tarba ya sha ta hanyar shan mama wanda wannan akwa illa a gare shi sosai dan za ta iya janyo mai wani abu na daban.

Leave a Comment