Abinda Ya Sa Na Daina Wakar Fadakarwa Da Nishadi –Abdulrahman Alfazazi

ABDURRAHMAN ALFAZAZI ya na daya daga cikin fitattun mawaka da su ke tashe a wannan lokacin musamman ma dai a bangaren wakoki na siyasa. Mawaki ne da ya ke da akida a fage sana’arsa ta waka, domin kuwa idan ban da wakokin yabon Manzon Allah (SAW) da na nishadi duk wakokin sa na siyasa ya tsaya ne ga bangaren jam’iyyar da Buhari yake cikinta tun da ya fara bai taba yin rawa ba.

 Domin jin irin yadda Alfazazi ya ke gabatar da wakokinsa da kuma yadda a ka yi ya samu lakabin Alfazazi, LEADERSHIP A YAU LAHADI ta tattauna da shi. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar tamu ta kasance, kamar haka: Da farko za mu so ka fadawa masu karatunmu sunanka da ma yadda aka yi ka zama Alfazazi. 

To da farko dai sunana Abdurahman Ayuba wanda aka fi sani da Alfazazi, kuma yadda aka yi na samu lakabin Alfazazi a kullum ina fada Allah ne ya sa aka samu wani dace wanda shi mawallacin littafin Ishriniyya wato Sheikh Alfazazi sunansa Abdurahman kuma ake yimasa lakabi da Alfazazi wanda ya ke mutumin Andulus ne. to akwai maigidana Alhaji Munir Garba mai sikeli wanda shi ne a sa na rubuta wata waka ta marigayi Sarkin Kano Ado Bayero sai na yi mata tsarin baituka kamar yadda shi mai ishiriya yake yi, idan ya yi dango na hudu sai ya sauka a na biyar.

 To da na gama na kai masa rubutun ya gani sai ya ce kai wannan rubutun kamar rubutun ishiriniya? To da na je aka buga wakar ya ji sai ya ce ka yi wata waka sai ka ce Alfazazi. Daga yanzu ma sunan ka Alfazazi. To wannan shi ne asali yadda na samo sunan Alfazazi. An san ka da wakok kala-kala. Ko za ka fada mana irin bangarorin da kake yi wa waka? To da farko dai na fara yin wakoki ne na yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) daga baya na yi wakar fadkaarwa na yi wakar zumunci, Halin Zuciya, na yi wakar Zamantakewa kuma sune dai wakokin da na yi na fadakarwar, sannan kuma ina yin wakokin biki.

 Daga karshe ina yin wakokin siyasa wanda a yanzu su na fi baiwa karfi. To me ya sa a yanzu ka daina wakoki sai na siyasa kadai? Eh to, na ji dadin wannan tambaya, domin kuwa abin da ya sa na daina wakokin fadakarwa da wakokin da na ke yi na nishadi shi ne na fadada tunanina musamman kan halin da duniya take ciki kamar ma kasarmu Nigeria domin yanzu ba maganar sauraron wakar Album ko ku ma kallon bidiyo ake yi ba, yanzu abin da yake gaban mutane shi ne a samu ingantaccen tsaro, wutar lantarki, ta tsaya, a samu zaman lafiya ingantacce, to kuma abin farin ciki duk wadannan matakan an dauko hanya da zarar an gama zaben nan za ka ga komai yana tafiya hankalin mutane ya kwanta. To daga wannan lokacin ne zan ci gaba da yin wakokina na fadakarwa don fadakar da mutane da ku ma nishadantar da su. 

To ya za ka kwatanta bambancin dake tsakanin wakokin siyasa da kuma wanda ka saba yin sa a baya? E akwai bambanci sosai. Domin wakar yabon Annabi ita ce take sa kamala, su kuma wakokin da sue shafi na fadakarwa da kuma na finafinai sun fi sa mutum ya yi suna lokaci guda. Amma kuma wakar da za a samu kudi to babu kamar wakar siyasa. Don haka kowanne bangaren akwai nasa abinda ake samu

. Kenan dai a yanzu za a iya cewa Alfazazi ya yi kudi ya bar fadakarwa da nishadatarwa? A’a ba bin kudi na yi ba, kamar yadda na fada aka na jingine sakamakon wadandan dalalai kuma ina yin wakar siyasa ne ba don komai ba sai on ina kishin kasata, domin haka nake bada gudunmawata don a kawo canji wanda in hakan ya samu to mu ma muna cikin ladan don haka ne na bada karfi wajen wakar siyasa don na ba da tawa gudunmawar.

 Saidai tun da aka san ka a wakar siyasa an san ka ne a layi daya ba kamar sauran mawaka da ake yin su a ko’ina ba. To wannan dalili shi ne duk lokacin da na kulla amana da kai na yarda cewa ina tare da kai to ko wani ya zo ya ce zai ba ni wani abu to zan ce na riga na yi alkawari. Don haka da dadi ba dadi ba zan canja ba ko da mulki ko ba mulki ina tare da shi. ko zai ba ni ko ba zai ba ni ba don alkawari na dauka ina nan a kan sa.

 Akwai wata dabi’a ta mawakan siyasa musamman ma kalamai na cin zarafi da suke yi. Kana ganin wannan abu ne da ya dace? To gaskiya wannan ba abu ne da ya dace ba, domin kuwa ita kanta siyasayar bai kamata a dauke ta ko a mutu ko a yi rai ba. Domin kuwa wani lissafi ne wanda ake so ka jawo makiyi ya zama masoyi. To idan ka zagi makitika a ca sa gobe wata tafiyar ta hada ku ya shigo layin wanda kake so, to da wanne ido za ka kalle shi? don haka ba abu ne mai kyau ba mawaka na siyasa mu rinka batanci don wannan ba abu ne mai kyau ba muna fatan za mu gyara. Idan aka duba a baya mawakan siyasa sun fi kima da daraja ko me ya sa a yanzu ba su da kima kamar a baya? Haka ne, na farko akwai rahsin akida da rahsin alkibla, kamar yadda na fada ma ni idan na yi alkawari da mutum to babu wani matsi na rayuwa da zai s ana canja ko na zagi wanda nake tare da shi. idan mawaka suna haka zai sa ka ga ana jin tsoron mu. 

To amma a yanzu sai ka ji su mawakan suna cewa harshen fa da ya yi yabo zai iya yin zago. To ka ga wanan bai kamata ba. Kuma wannan bain ne yake ba mu matsala. To ko akwai wani sharadi da kake da hsi idan mutum ya zo yana son ka yi masa waka? Sosai ma kuwa. Inda sharadi don na farko ma sai na tambaye ka a wacce jam’iyya kake? Domin ni dan APC ne jam’iyya nake yi wa aiki, idan ka fada min jam’iyyar ka na ji ba tawa ba ce sai na ce ka yi hakri sia dai na nemo maka wane shi zai iya yi maka, amma ni an san ni a jam’iyyata kuma na dau alwakarin ba zan canja ba, don haka ni ba za a ba ni kudi na yi wa wata jam’iyya waka ba, amma zan iya yi saboda neman masalaha misali kamar Jihar da ba tamu ba aka ce ga dan takara daga jam’iyya kaza to sia na duba me ya yi wa mutane idan na ga nagartarsa to zan iya yi masa ba tare da na soki wani ba.

Ko mene ne sakon ka na karshe? To saokna abin d anake so mawaka su gane mu ji tsoron Allah mu tsaya kaifi daya domin haka ne zai sa mu tafi da kimar mu da mutuncinmu. To madalla mun gode. Ni ma na gode. 

No comments

Powered by Blogger.